Ma’aikatar tsaron Amurka ta bayyana Iran ta yi yunkurin kashe shugaban Amurka Donald Trump, inda ta kara da cewa sojojin Amurka sun kashe wani jami’in Iran ɗin da ake zargi da jagorantar shirya wannan yunkuri.
Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ne ya sanar da hakan a yayin da yake magana da ‘yan jarida a hedkwatar ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon,
Ya ce, “Iran ta so ta kashe Shugaba Trump, amma daga karshe Trump ne ya yi nasara.”
A shekarar 2024 kuwa, gwamnatin Amurka ta gurfanar da wani dan asalin Afghanistan bisa zargin hannu a wani shiri da ake zargin Iran ta shirya na kashe Trump kafin ya fara aiki bayan nasararsa a zaɓen waccan shekarar.
Tsohon babban lauyan gwamnatin Amurka Merrick Garland shima ya ce ma’aikatar shari’a ta tuhumi “wani mutum da ke aiki wa gwamnatin Iran wanda aka ɗora wa alhakin jagorantar masu aikata laifi domin aiwatar da shirin kashe wasu mutane, ciki har da Donald Trump.”
Sai dai Iran ta musanta wadannan zarge-zargen.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce an taɓa irin wadannan zarge-zarge kan ƙoƙarin kashe shugabannin Amurka a baya, amma Iran ta ƙaryata su, yana mai cewa daga baya an gano cewa ba gaskiya ba ne.