Ofishin Jakadancin Amurka da ke birnin Abuja ya sanar da rufe aikinsa na yau da kullum na wucin gadi, sakamakon yiwuwar barkewar zanga-zanga a babban birnin tarayyar, biyo bayan yaƙin Amurka da Iran
A wata sanarwa da Ofishin ya wallafa a shafinsa na X, ya ce za a rufe ofishin har zuwa ranar Litinin, 9 ga Maris, 2026.
Sanarwar ta ce:
“Saboda yiwuwar zanga-zanga a Abuja, Ofishin Jakadancin Amurka zai kasance a rufe ga ayyukan yau da kullum har zuwa Litinin, 9 ga Maris, 2026.
“An dage dukkan alƙawuran neman biza da aka tsara yi a ranakun 4 da 5 ga Maris, tare da alƙawuran Sashen Kula da ‘Yan Ƙasar Amurka (ACS) na ranar 5 ga Maris, kuma an mayar da su zuwa mako mai zuwa.”
Wannan mataki dai na zuwa ne bayan rahotanni sun nuna cewa an tsaurara matakan tsaro a sassa daban-daban na Abuja sakamakon yiwuwar zanga-zangar mambobin ƙungiyar (IMN) don nuna kin jinin kisan da Amurka da Isra’ila suka yiwa jagoran addinin Iran Ayatullah khamene’i.