Ana ci gaba da makokin mutane aƙalla 30 da suka rasa rayukansu a wani mummunan haɗarin mota da ya faru a jihar Kano ta Arewacin Najeriya bayan da wata babbar motar dakon kaya ta kufce tare da bi takan motocin safa.
Haɗarin mota ba sabon abu ba ne a Najeriya inda a lokuta da dama ya kan haddasa asarar ɗimbin rayuka.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a kan babbar hanyar Kwanar Barde da ke ƙaramar hukumar Gezawa mai gajeruwar tazara da tsakar birnin Kano, inda babbar motar dakon kayan ta niƙe motar safa kuma nan ta ke mutane 30 suka mutu yayinda wasu da dama suka jikkata.
Haɗarin wanda ke sahun mafi muni da jihar Kano ta gani a baya-bayan ya tashi hankali mutane da dama inda aka jiyo Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf na aikewa da saƙon ta’aziyya ta cikin wata sanarwa da mai magana yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta bayyana kaɗuwar Gwamnan da samun bayani kan haɗarin inda ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa tare da jajantawa waɗanda suka jikkata.
Sanarwar ta ruwaito Gwamnan ya yi umarnin baiwa dukkanin waɗanda suka jikkata a haɗarin kulawar lafiya kyauta.
Yawancin hadura na faruwa ne saboda lalacewar hanya ko kuma gangancin masu tuƙi ba sabon abu ba ne a sassan Najeriya inda a shekarar 2025 da ta gabata hukumar kiyaye afkuwar haɗurra ta ƙasar wato FRSC ta sanar da samun haɗurra dubu 10 da 446 a sassan Najeriyar wanda ya sabbaba mutuwar mutane dubu 5 da 289.