Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya karɓi baƙuncin kwamandan sojojin Amurka a Afirka.

Tinubu ya karɓi baƙuncin kwamandan sojojin Amurka a Afirka.

Tinubu ya gana da shugaban dakarun Amurka na Afirka.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi wata tawaga daga ƙasar Amurka ƙarƙashin jagorancin Kwamandan rundunar sojin Amurka a Afirka USAFRICOM an Abuja.

Janar Dagvin R. Anderson ne ya jagoranci tawagar, tare da rakiyar Muƙaddashin Jakadan Amurka a Najeriya, Mista Keith Heffern da sauran jami’ai.

Shugaba Tinubu ya tarbi baƙin tare da mai ba shi shawara kan tsaro, Mallam Nuhu Ribadu da shugabannin rundunonin tsaron Najeriya.

Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa kan Harkokin Sada Zumunta, Mista Dada Olusegun, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Ko da yake ba a bayyana cikakkun bayanai kan abin da aka tattauna a ganawar ba, ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka ke ƙara ƙarfi.

Haka kuma, ganawar ta biyo bayan wasu rahotannin da suka nuna cewa Amurka ta tura ƙaramin rukuni na sojojinta zuwa Najeriya a ranar 3 ga Fabrairu, lamarin da ya zama karon farko da aka amince a hukumance da kasancewar sojojin Amurka a ƙasar tun bayan hare-haren sama da aka kai kan sansanonin yan ta’adda a ranar Kirsimetin shekarar 2025.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments