Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNLC ta shirya zanga-zanga kan rufa rufar dokar zabe

NLC ta shirya zanga-zanga kan rufa rufar dokar zabe

NLC ta yi barazanar fita zanga-zanga kan ɓoyayyen sauya dokar zaɓe.

Babbar ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, NLC ta yi gargaɗin gudanar da zanga-zangar a faɗin ƙasar tare da barazanar ƙaurace wa zaɓukan ƙasar masu zuwa kan abin da ta bayyana da ‘rashin tabbas’ game da bayanan da ke cin karo da juna game da gyaran dokar tura sakamakon zaɓe ta na’ura.

Cikin wata sanarwa da NLC ta fitar, ƙungiyar zargi Majalisar Dattawa da kashe jikin jama’a kan tsarin zaɓen Najeriya ta hanyar kasa bayyanawa ƙarara kan cewa ko aika sakamakon zaɓen ta na’ura zai zama tilas.

“NLC ta bayyana matuƙar damuwarta kan halin rashin tabbas da bayanai masu cin karo da juna da ke fitowa daga majalisar dattawan Najeriya game da gyaran fuskar da aka yi wa dokar zaɓen ƙasar ta 2022, musamman dokar wajabta aika sakamako ta na’ura,” kamar yadda shugaban ƙungiyar Joe Ajaero, ya bayyana cikin sanarwar.

Ƙungiyar ta ce rashin fayyacewa ƙarara da ke tattare da amincewa majalisar tattawan na barazana ga sahihanci zaɓuƙan masu zuwa.

Haka kuma NLC ta ce ƴan Najeriya sun cancanci samun bayanai, inda za su ci gaba da ganin sakamakon ƙuri’unsu bayan ƙirga su.

A wannan makon ne majalisar dattawan ƙasar ta amince ta gyaran dokar zaɓen, sai dai an riƙa samun bayanai masu cin karo da juna musamman kan dokar wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments