Jam’iyyar PDP ta yi gargaɗin cewa ɓangaren Tanimu Turaki zai ɗauki duk wasu matakai na shari’a domin ƙalubalantar abin da suka kira da yankan baya.
A farkon wannan makon ne dai hukumar zaɓen ƙasar INEC ta amince da kwamitin riƙon ƙwarya da Nyesome Wike ke goyon baya cewa shi zai samar da shugaban jam’iyya na riƙo da sakataren jam’iyya da sakataren tsare-tsare dukansu daga ɓangaren Nyesome Wike a matsayin waɗanda ta amince su halarci taron tattaunawar jam’iyyar na rubu’in shekara da zai gudana a Abuja.
Cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar a ranar Alhamis ta ce ta yi watsi da matakin.
Sai dai jam’iyyar PDP ƙarƙashin shugabancin Kabiru Tanimu Turaki dai ta yi watsi da matakin na hukumar zaɓen Najeriyar, inda ta ce kundin tsarin jam’iyyar PDP ma bai yi wannan tanadi ba, kuma ba shi da hurumi a doka.