Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTrump ya jajanta wa Najeriya kan harin da aka kai Jihar Kwara

Trump ya jajanta wa Najeriya kan harin da aka kai Jihar Kwara

Ofishin jakadanci Amurka a Najeriya ya fitar da wata sanarwa a yau Juma’a inda ya yi Alla-wadai da “mummunan harin da aka kai a jihar Kwara” da ke Arewacin Najeriya, inda aka kashe mutanen da har yanzu ba a kammala tantance yawansu ba.

A cikin sanarwar da ofishin ya fitar a shafukan sada zumunta ta ce “muna miƙa alhininmu ga iyalan waɗanda wannan kisa na rashin hankali ya shafa, kuma muna maraba da matakin shugaba Tinubu na tura dakaru domin tsare ƙauyukan da ke yankin”.

A ranar Talatar ne dai wasu mahara da ake zargin masu tsattsauran ra’ayin addini ne suka kai hari kan ƙauyukan Woro da kuma Nuku a ƙaramar hukumar Kaiama da ke jihar Kwara, inda suka kashe mutanen da ake hasashen sun zarta 100.

Shugaban ƙasar, Bola Tinubu dai ya ɗora alhakin harin kan ƙungiyar Boko Haram wadda ta shafe sama da shekara 15 tana kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

A baya-bayan shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ana yi wa mabiya addinin Kirista a Najeriya kisan gilla, lamarin da gwamnatin ƙasar ta musanta.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments