Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTrump ya janye bidiyon da ke nuna cin mutuncin Obama ta launin...

Trump ya janye bidiyon da ke nuna cin mutuncin Obama ta launin fata

Trump ya goge wani bidiyo da ke ɗauke da nuna wariyar launin fata ga Obama.

Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya cire wani bidiyo da aka wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta wanda ke nuna wariyar launin fata ga Barack Obama da Uwargidansa Michelle inda aka nuna su a matsayin birai.

Hotonunan dai sun kasance a ƙarshen wani bidiyo na daƙiƙa 62 da ke iƙirarin an tafka maguɗin zaɓe a zaben shugaban ƙasa na 2020.

Da yake magana da manema labarai a ranar Juma’a, Trump ya ce: “Ban yi kuskure ba”.

Ya ƙara da cewa farkon bidiyonne kawai kafin wani ma’aikaci ya wallafa shi kuma bai san yana ɗauke da wannan hoton na Obama ba.

Sanata Tim Scott na jam’iyyar Republican, ya yi kira ga shugaban kasar da ya cire bidiyon, yana mai bayyana shi a matsayin “abin nuna wariyar launin fata mafi muni da na gani daga fadar ta White House”.

Bayan sukar da fadar White House ta sha kan lamarin, ciki har da wasu ƴan majalisar dattawan ƴan jam’iyyar Republican, an cire bidiyon daga shafin Trump na dandalin ‘Truth Social’ inda aka ce wani jami’in gwamnatin ne ya wallafa bidiyon bisa ‘kuskure’.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments