Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Masarautar Saudiyya sun sake jaddada aniyarsu ta ƙarfafa haɗin guiwa a harkokin gudanar da Hajji da Umrah, biyo bayan wani muhimmin taro da manyan jami’an ƙasashen biyu suka gudanar an Abuja.
Mai taimakawa Shugaban NAHCON a bangaren yada labarai, Ahmad Mu’azu, ya ce taron ya haɗa hukumomin Najeriya da wata tawaga daga Saudiyya ƙarƙashin jagorancin Ministan Hajji da Umrah na Masarautar Saudiyya, Dakta Tawfiq Al-Rabiah.
An bayyana ziyarar a matsayin wata muhimmiyar alama ta ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman wajen kula da alhazan Najeriya.
Shugaban Hukumar Kula da Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Usman, ya ce ziyarar ta nuna ci gaba da haɗin guiwar Saudiyya da Najeriya wajen yi wa Baƙin Allah hidima.
Ya yaba wa Masarautar bisa ƙoƙarinta na inganta jin daɗin alhazai da samar da ababen more rayuwa da tabbatar da tsaro da kuma inganta ayyukan Hajji da Umrah, musamman ta hanyar shirin Saudi ‘Vision 2030’.
Farfesa Abdullahi Usman ya gamsu cewa akwai wasu ƙalubale da suka shafi bizar Umrah ga ’yan Najeriya, musamman matsalar tsawaita zama bayan wa’adin izini daga wasu alhazai.
Ya jaddada cewa Najeriya za ta yi aiki kafada da kafada da hukumomin Saudiyya domin shawo kan matsalar, ta hanyar tsaurara sa ido kan kamfanonin da ke da lasisi da inganta tsarin bayanai da kuma wayar da kan allumma.
Ya kuma tabbatar da cewa NAHCON za ta bi duk ƙa’idoji da umarnin Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya, tare da kare mutuncin harkokin Hajji da Umrah da muradun alhazan Najeriya.