Amurka ta sabunta yarjejeniyar da za ta bai wa ƙasashen Afrika 32 damar kasuwancin da bashi da ba shinge a kasuwannin ƙasar.
Yarjejeniyar irin wannan kasuwancin da aka cimma ta ƙare ne tun a watan Satumbar da ya gabata bayan ta shafe shekara 25 tana aiki.
Yanzu, an sabunta ta har zuwa ƙarshen shekarar 2026.
Ministan kasuwanci na Amurka ya ce zai yi aiki tare da ‘yan majalisar dokokin ƙasar domin sake yi wa yarjejeniyar garanbawul.