Ana sa ran Ukraine da Rasha za su fara tattaunawa ta tsawon kwanaki biyu nan ba da jimawa ba, domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Abu Dhabi.
Amurka ce ta shirya tattaunawar a wani yunƙuri na kawo ƙarshen yakin da ke ci gaba da gudana tsakanin ƙasashen biyu.
A jiya Talata, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da zaɓar yaƙi maimakon zaman lafiya, biyo bayan sabon harin da aka kai wa ƙasarsa.
Ya kuma yi kira da a ƙara matsa wa Rasha lamba a duniya, domin tilasta mata amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya.
Sai dai a halin yanzu, Ukraine na fuskantar matsin lamba daga Amurka, wadda ke buƙatar ta sassauta matsayinta ta hanyar miƙa wasu yankunanta da aka ƙwace a gabashin yankin Donbas, domin cimma zaman lafiya.