Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya rantsar da shugabar hukumar FCC da kwamishinoni 37

Tinubu ya rantsar da shugabar hukumar FCC da kwamishinoni 37

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rantsar da Shugabar Hukumar tabbatar da daidaito ta FCC da kuma kwamishinonin hukumar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis.

Sabuwar Shugabar FCC, Hulayat Omidiran, ta karɓi rantsuwar kama aiki tare da kwamishinoni 37 da ke wakiltar jihohi 36 na ƙasar nan da kuma babban birnin tarayya Abuja da misalin ƙarfe 4:48 na yamma.

Omidiran mai shekaru 59, tsohuwar ‘yar majalisar wakilai ce wacce ta wakilci mazabar Ayedaade/Irewole/Isokan ta Jihar Osun daga shekarar 2011 zuwa 2019. yayin da ta gaji Dr. Muheeba Dankaka, wadda fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa wa’adinta ya kasance cike da cece-kuce.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments