Sunday, October 18, 2026
HomeTsaroƳan daba sun bi dare, sun cinna wuta a unguwar Kano

Ƴan daba sun bi dare, sun cinna wuta a unguwar Kano

Rahotanni sun ce yan daban sun jefa jama'a a cikin firgici

Al’ummar unguwar Rijiya Biyu da ke ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano sun kwana cikin tsananin fargaba, bayan wasu ɓatagari sun cinna wuta a wurin sayar da karan yin gurasa da ke yankin.

Rahotanni sun nuna cewa tarin ƴan daba ne suka shiga unguwar cikin dare ɗauke da makamai, inda suka cinna wa wajen karan wuta, tare da kai wa mutane sara da barazana.

Shaidun gani da ido sun ce wutar ta bazu sosai, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin ruɗani da firgici, inda suka rika neman agaji domin hana wutar ta ƙara yaduwa.

Hotuna da bidiyo da mazauna unguwar suka yaɗa a kafafen sada zumunta cikin dare sun nuna girman wutar da yadda ta rika ci, yayin da jama’a ke ƙoƙarin tsira da dukiyoyinsu.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani daga jami’an tsaro kan musabbabin lamarin ba, haka kuma ba a bayyana ko an kama wasu daga cikin waɗanda ake zargi ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments