Allah SWT ya karɓi rayuwar ɗaya daga cikin fitattun malaman Sunnah, Sheikh Habibu Yahaya Kaura, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Aiki na JIBWIS Nigeria.
Rahotanni sun tabbatar da cewa malamin ya rasu ne a safiyar yau Laraba 21 Janairu, 2027 bayan jinya da ya shafe wani lokaci yana fama da ita.
Za a gudanar da sallar jana’izarsa a ranar Laraba, 2 Sha‘aban 1447H dai-dai da 21/01/2026 da karfe 4:30 na yamma, bayan sallar La’asar.
Za a yi sallar a Masallacin Umar bn Khattab, Dake, Utako Berger Junction,Hedikwatar IZALA ta Ƙasa, Abuja