Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiDSS ta sake kama Malami bisa zargin tallafa wa ta'addanci

DSS ta sake kama Malami bisa zargin tallafa wa ta’addanci

Hukumar DSS a kuma kama Malami kan zargin ta’addanci

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta kama tsohon babban lauya Najeriya kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami.

Wata majiya mai tushe daga hukumar ta tabbatar da cewa DSS ta kama shi ne bisa zargin tallafa wa ta’addanci, bayan gano makamai da harsasai a gidansa da ke birnin Kebbi.

A wata sanarwa da wani makusanci tsohon Ministan, Honorable Abubakar B Sabo, tsohon ɗan majalisar Birnin Kebbi, ya tabbatar da kamen Malami.

An kama Malami wanda ake tuhuma a gaban wata babbar kotun tarayyar Abuja kan zargin halasta kuɗin haram a ranar Litinin jim kaɗan bayan an sake shi daga gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Jami’an gidan gyaran halin sun tabbatar da sakin Malami bayan cika sharuɗan beli.

A ranar 7 ga watan Janairu, 2026, Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarkashin jagorancin alƙali Emeka Nwite ta amince da bayar da belin tsohon Ministan shari’a Abubakar Malami da iyalinsa kan kuɗi Naira miliyan 500 da kuma mutum biyu da za su tsaya musu.

A cewar alƙalin, mutanen da za su tsaya musu sai sun kasance suna da filaye a yankunan Asokoro da Maitama ko Gwarinpa, sannan kuma sai sun miƙa dukkan takardun tafiyarsu ga kotu.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments