Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Kano za ta jagoranci shigar da kara kan kisan da aka...

Gwamnatin Kano za ta jagoranci shigar da kara kan kisan da aka yi wa wasu iyalai a Dorayi

Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta jagoranci shigar da ƙara kan kisan gillar da aka yi wa wata matar aure da ƴaƴanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke birnin Kano, lamarin da ya jefa al’ummar jihar cikin alhini da girgiza.

A cikin wata sanarwa da babban lauyan jihar kuma kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN ya fitar, ya ce bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf, gwamnatin jihar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da daukacin al’ummar Kano.

Gwamnatin ta yaba wa rundunar ƴan sandan jihar bisa gaggawar ɗaukar matakin bincike da ya kai ga kama manyan waɗanda ake zargi da aikata laifin.

Gwamnatin ta jaddada cewa za a gudanar da shari’ar cikin gaggawa da ƙwarewa ta hannun Ofishin Babban Lauyan Jihar, inda za a kafa tawagar lauyoyi ta musamman domin tabbatar da adalci.

SourceNasara
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments