Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana takaicin sa kan kisan gilla da aka yi wa wata matar aure mai suna Fatima Abubakar, da ƴaƴanta shida a unguwar Chiranci da ke Jihar Kano.
A cikin wata sanarwa da fadar, Shugaba Tinubu ta fitar ya bayyana lamarin a matsayin mummunan rashin imani da rashin tausayi, wanda ya girgiza al’umma da ma ƙasa baki ɗaya kuma ya saɓa wa hakkin Dan Adam.
Tinubu ya nuna mutukar alhini kan wannan mummunan lamari, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan.
Shugaban ya kuma yaba wa rundunar ƴan sandan Najeriya bisa gaggawar ɗaukar matakin da ya kai ga kama manyan waɗanda ake zargi da aikata laifin.
Ya kuma umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a cikin kisan a gaban kotu.