Majalisar Sarkin Musulmi ta umarci Musulmai su fara duban jinjirin watan Sha’aban 1447AH a ranar Litinin, 19, Janairu, 2026.
An bayyana sanarwar ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato kuma Shugaban Kwamitin Shawarwari kan Harkokin Addini, Farfesa Sambo Junaidu, ya sanya wa hannu.
Rahotanni sun bayyana cewa sanarwar ta ce ranar Litinin ta zo daidai da 29 ga watan Rajab 1447AH, wanda a bisa koyarwar Musulunci ita ce ranar da ake duba jinjirin wata.
Kwamitin Shawarwari kan Harkokin Addini ya bayyana cewa ayyana ranar duban jinjirin watan Sha’aban ya dace da al’adar Musulunci wadda ke bukatar a tabbatar da ganin wata kafin shiga sabon wata.
A cikin sanarwar, kwamitin ya jaddada cewa duban jinjirin wata a ranar 29 ga Rajab 1447AH ya dace da koyarwar Musulunci, inda za a tabbatar da shigowar Sha’aban ta hanyar gani ko cikar kwanaki 30.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa wannan mataki ba sabon abu ba ne, ci gaba ne da bin tsarin da fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ke bi a duk lokacin da ake dab da fara sabon watan Hijira.
Majalisar Sarkin Musulmi ta yi kira ga al’ummar Musulmi da su duba jinjirin wata da niyyar yin aikin addini. Kwamitin ya bukaci kowa da kowa da ya ga jinjirin watan da ya gaggauta kai rahoto ga hakimin gundumarsa ko kauyensa.