Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroƳan ta'adda sun kashe limami bayan sace shi a Katsina

Ƴan ta’adda sun kashe limami bayan sace shi a Katsina

Lamarin ya faru ne duk da yarjejeniyar zaman lafiya a Dandume da Faskari

Wasu ’yan bindiga sun kashe Alaramma Malam Sani, limamin babban masallacin Juma’a na garin Mahuta da ke ƙaramar hukumar Dandume a jihar Katsina, bayan sun sace shi a yammacin ranar Asabar.

Rahotanni sun ce an sace limamin ne yayin da yake dawowa daga ziyartar mahaifiyarsa a Kadisau, ƙaramar hukumar Faskari.

A ranar yau (Litinin) kuma aka tabbatar da mutuwarsa a hannun masu garkuwa da shi.

Bakatsine, Mai sharhi kan al’amuran tsaro a Arewa maso Yamma ta wallafa a shafin X cewa lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin alhini, musamman ganin cewa Dandume da Faskari na cikin ƙananan hukumomin da aka ce an cimma yarjejeniyar zaman lafiya a cikinsu.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro na ci gaba da bincike kan lamarin.Is this conversation helpful so far?

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments