Sunday, October 18, 2026
HomeKasashen wajeAmurka ta kai Maduro da matarsa kotu da ke New York

Amurka ta kai Maduro da matarsa kotu da ke New York

Shugaban Venezuela Nicola Maduro da mai ɗakinsa na kan hanyarsu ta isa wata kotu a birnin New York, kwanaki biyu bayan da sojojin Amurka suka kama su a wani hari da suka kai Caracas.

Za a yi musu shari’ah ne bisa zarginsu da safarar muggan ƙwayoyi da kuma ta’addanci, laifukan da a baya suka musanta

A Venezuela kuwa, anjuma a yau ne za a rantsar da Delcy Rodriguez a matsayin shugabar riƙo ta Venezuela.

Gabanin taron shan rantsuwar a majalisar dokokin ƙasar, Miss Rodriguez ta wallafa a shafinta na sada zumunta cewa gwamnatinta na da niyyar ƙulla alaƙa ta mutuntaka da haɗaka da Amurka.

Sai dai mista Trump ya sake jaddada cewa a yanzu haka Amurka ce ke da iko da Venezuela.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments