Thursday, November 12, 2026
HomeLabarai’Yan daba sun kai hari kan gangamin kamfen ɗin Pantami a Gombe

’Yan daba sun kai hari kan gangamin kamfen ɗin Pantami a Gombe

Wasu matasa da ake zargin ’yan daba ne sun cinnawa tayoyi wuta a kan titin Jekadafari, kusa da gidan iyalan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, domin hana ɗan takarar gwamnan Gombe na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, shiga cikin birnin.

Wasu matasa da ake zargin ’yan daba ne sun cinnawa tayoyi wuta a kan titin Jekadafari, kusa da gidan iyalan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, domin hana ɗan takarar gwamnan Gombe na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, shiga cikin birnin.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, lokacin da Pantami ke kan hanyarsa ta zuwa babban birnin jihar domin halartar gangamin siyasa da liyafar tarbar sa da jam’iyyar PDP ta shirya.

Shaidun gani da ido sun ce matasan, waɗanda ake zargin magoya bayan APC ne, sun tare hanya da tayoyi kafin su cinna musu wuta. Hakan ya jefa masu ababen hawa da mazauna yankin cikin fargaba, tare da kawo cikas ga zirga-zirga.

Rahotanni sun ce wasu ’yan kasuwa sun rufe shagunan su saboda tsoron rikicin siyasa. Duk da haka, ayarin motocin Pantami da ya ƙunshi daruruwan motoci ya samu damar wucewa ta wurin tare da ci gaba da tafiya zuwa wajen taron.

A yayin da ayarin ke wucewa, wasu matasa ɗauke da makamai sun far wa motocin da ke cikinsa, inda suka farfasa gilasan wasu daga cikinsu. Sai dai jami’an tsaro da aka tura yankin sun shiga tsakani tare da dawo da zaman lafiya.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa da Pantami ko hadimansa suka fitar kan lamarin. Haka kuma, rundunar ’yan sandan jihar ba ta fitar da sanarwa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments