Tuesday, November 10, 2026
HomeLabaraiAn sace fanal 25 na saman masallacin Kanzul Mudalsam a Kano

An sace fanal 25 na saman masallacin Kanzul Mudalsam a Kano

Wasu da ake zargin ɓarayi ne sun sace fanal guda 25 a saman masallacin Kanzul Mudalsam da ke unguwar Gwammaja, a kan titin Katsina a cikin birnin Kano.

Wasu da ake zargin ɓarayi ne sun sace fanal guda 25 a saman masallacin Kanzul Mudalsam da ke unguwar Gwammaja, a kan titin Katsina a cikin birnin Kano.

Jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Dala, Sagiru Nazifi Yakasai, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa mai kwanan watan 9 ga Nuwamba, 2026.

Sanarwar ta ruwaito bayanin Alhaji Salisu Sabon Titi, wani hadimi kuma ɗan ƙungiyar Gwammaja Inafita, wanda ya ce satar kayayyaki da fadan daba sun zama ruwan dare a yankin.

Ya bayyana cewa masu aikata laifukan ba wai fitilu kawai suke sata ba, har ma suna lalata turakun da aka ɗora su a kai.

Ya ƙara da cewa matsalar tsaro ta jefa mazauna yankin cikin fargaba, inda wasu ke tsoron bin hanyoyin yankin bayan ƙarfe shida na yamma. A makon da ya gabata ma, an sace babura biyar tare da ƙwace wayoyin salula daga hannun mutane.

Alhaji Salisu ya yi kira ga gwamnatin Kano da hukumar yaƙi da shaye-shaye da fadan daba, ƙarƙashin jagorancin Muhyi Magaji Rimin Gado, da su gaggauta ɗaukar matakan magance matsalar domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments