Tuesday, November 10, 2026
HomeFasahaAn yi hasashen duniya za ta tashi ranar Juma’a mai zuwa

An yi hasashen duniya za ta tashi ranar Juma’a mai zuwa

Wani tsohon binciken kimiyya da aka wallafa shekaru 66 da suka gabata ne ya jawo sabon tashin hankali kan ikirarin cewa duniya za ta ƙare ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, 2026.

Wani tsohon binciken kimiyya da aka wallafa shekaru 66 da suka gabata ne ya jawo sabon tashin hankali kan ikirarin cewa duniya za ta ƙare ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, 2026.

Binciken, wanda masana kimiyya uku suka gudanar, an wallafa shi ne a mujallar Science ta Amurka a ranar 4 ga Nuwamba, 1960, da taken “Doomsday: Friday, November 13”.

Masu binciken, Heinz von Foerster, Patricia Mora da Lawrence Amiot, sun yi amfani da bayanan tarihin yawan al’ummar duniya domin hasashen yadda yawan jama’a zai ci gaba da ƙaruwa.

Sun yi hasashen cewa idan aka ci gaba da samun irin wannan saurin ƙaruwa ba tare da wani sauyi ba, yawan al’ummar duniya zai kai wani matsayi da ba shi da iyaka a lissafi a tsakiyar watan Nuwamba na shekarar 2026.

Sai dai binciken bai yi hasashen cewa bil’adama za su mutu ko kuma wata masifa za ta hallaka duniya a ranar ba. Kalmar “Doomsday” da aka yi amfani da ita tana nufin wani matsayi ne na lissafi da ke nuna ƙarshen ingancin wannan tsarin hasashe.

Masu binciken sun kuma fahimci cewa abubuwa kamar ƙarancin albarkatu, yanayin muhalli, haihuwa da mace-mace na iya sauya yadda yawan jama’a ke ƙaruwa.

Haka kuma, an sake tayar da batun ne bayan wasu kafafen yaɗa labaran Masar sun sake wallafa wani tsohon rahoto na shekarar 1964, wanda marubuci Michel Tecla ya rubuta, yana iƙirarin cewa duniya za ta ƙare a wannan rana.

Wasu rahotannin sun kuma danganta ranar da ayyukan rana da yiwuwar guguwar rana, wadda za ta iya shafar sadarwa, tauraron ɗan Adam da tsarin samar da wutar lantarki.

Sai dai binciken da aka wallafa a mujallar Science bai bayar da wata hujja da ke danganta ranar 13 ga Nuwamba da ayyukan rana ko wata babbar masifa ta halitta ba.

A sakamakon haka, babu wani tabbaci a cikin wannan binciken da ke nuna cewa duniya za ta ƙare ranar Juma’a 13 ga Nuwamba, 2026.

SourceBBC,
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments