Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiAtiku Abubakar ya kai ziyarar girmamawa ga Sarkin Musulmi a Sakkwato

Atiku Abubakar ya kai ziyarar girmamawa ga Sarkin Musulmi a Sakkwato

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya kai ziyarar girmamawa ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, a fadarsa da ke birnin Sakkwato.

Tashar Siyasarmu TV ta ruwaito cewa Atiku ya kai ziyarar ne tare da wasu mambobin tawagar jam’iyyar ADC, inda suka samu damar gaisawa da Sarkin Musulmi tare da girmama masarautar.

A yayin ziyarar, tawagar ta bayyana jinjinawarta ga gudunmawar da Sarkin Musulmi ke bayarwa wajen tabbatar da haɗin kan Najeriya, zaman lafiya da haƙurin addinai.

Haka kuma, sun yaba da rawar da yake takawa wajen ƙarfafa zumunci da zaman tare tsakanin al’ummar ƙasar, tare da bayyana shi a matsayin uba mai muhimmiyar gudunmawa wajen samar da zaman lafiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments