Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiSanata Barau ne fitaccen mataimakin shugaban majalisa tun 1999 – Rahoto

Sanata Barau ne fitaccen mataimakin shugaban majalisa tun 1999 – Rahoto

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya gabatar da kudurori 48 cikin watanni 40 da ya shafe a majalisa ta 10, inda biyar daga cikinsu suka zama doka.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya gabatar da kudurori 48 cikin watanni 40 da ya shafe a majalisa ta 10, inda biyar daga cikinsu suka zama doka.

Kungiyar ’yan jarida masu ɗaukar rahotannin majalisar dattawa (SPC) ce ta ba shi lambar yabo ta fitaccen mataimakin shugaban majalisar dattawa tun bayan dawowar dimokuradiyya a 1999.

Shugaban kungiyar, Comrade Taye Odewale, ya ce sun yi la’akari da ayyukan majalisa, muhawara, sa ido kan hukumomi da wakilcin al’umma wajen tantance shi.

Daga cikin kudurorin da Barau ya gabatar akwai na kafa Hukumar Raya Arewa maso Yamma, Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Gwarzo, da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Kabo, a jihar Kano.

Bayan karbar kyautar an Abuja, Barau ya ce wannan karramawa za ta kara masa kwarin gwiwar yin aiki tukuru wajen karfafa dimokuradiyya da samar da dokokin da za su amfani al’umma, musamman mazabarsa ta Kano ta Arewa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments