Friday, November 6, 2026
HomeFasahaA kafa asusun dala biliyan 10 domin bunkasa fasahar AI a Afirka...

A kafa asusun dala biliyan 10 domin bunkasa fasahar AI a Afirka – Adesina

Tsohon shugaban Bankin Raya Afirka, Dr Akinwumi Adesina, ya bukaci kasashen Afirka su jagoranci bunkasa fasahar AI maimakon dogaro da fasahohin kasashen waje.

Tsohon shugaban Bankin Raya Afirka, Dr Akinwumi Adesina, ya bukaci kasashen Afirka su jagoranci bunkasa fasahar AI maimakon dogaro da fasahohin kasashen waje.

Ya bayyana hakan ne a taron shugabanci na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja, inda ya gabatar da shawarar kafa asusun dala biliyan 10 domin bunkasa fasahar AI a nahiyar.

Adesina ya ce asusun zai taimaka wajen jawo jarin dala biliyan 50 cikin shekaru 10, yana mai cewa Afirka ba za ta iya dogaro da kirkire-kirkiren kasashen waje ba.

Ya kuma bukaci a bunkasa kayayyakin more rayuwar zamani, samar da fasahohi a cikin gida da karfafa shugabancin siyasa wajen tafiyar da harkokin AI.

A nasa bangaren, Ministan Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Bosun Tijani, ya bayyana cewa Najeriya na shirin shimfida kilomita 90,000 na igiyoyin sadarwa da horas da kwararru miliyan uku.

Ya ce Najeriya ta kuma kaddamar da dabarun AI na kasa tare da samun matsayi na farko a Afirka wajen kula da harkokin fasahar bisa ka’idojin da suka dace.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments