Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiNAWOJ ta shiga jimami, ta yi ta'aziyyar rasuwar 'yar jarida Zainab Rabi'u...

NAWOJ ta shiga jimami, ta yi ta’aziyyar rasuwar ‘yar jarida Zainab Rabi’u Salisu

Ƙungiyar ’Yan Jarida Mata ta Najeriya (NAWOJ), reshen Jihar Kano, ta bayyana alhininta kan rasuwar ɗaya daga cikin mambobinta, Zainab Rabi’u Salisu.

Ƙungiyar ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalan marigayiyar, ’yan uwa, abokai, abokan aikinta da kuma daukacin mambobin NAWOJ bisa wannan babban rashi.

A cikin sanarwar ta’aziyyar, ƙungiyar ta bayyana cewa rasuwar Zainab babban rashi ne ba ga iyalanta da masoyanta kaɗai ba, har ma da harkar aikin jarida da sauran al’ummar kafafen yaɗa labarai.

NAWOJ Kano ta kuma bayyana cewa za a ji babban gibi sakamakon rasuwarta, musamman a tsakanin waɗanda suka san ta kuma suka yi aiki tare da ita.

Ƙungiyar ta yi addu’ar Allah Ya ba iyalanta da duk waɗanda wannan rashi ya shafa haƙurin jure wannan ƙaddara, tare da roƙonSa Ya gafarta mata kurakuranta, Ya karɓi kyawawan ayyukanta, Ya yalwata kabarinta, Ya sanya mata haske a cikinsa, Ya kuma karɓe ta cikin rahamarsa a Aljannatul Firdaus.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments