Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabaraiMajalisar Dokokin Kano ta tsawaita dakatarwar shugabannin kananan hukumomi uku

Majalisar Dokokin Kano ta tsawaita dakatarwar shugabannin kananan hukumomi uku

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ƙara tsawaita dakatarwar da ta yi wa shugabannin ƙananan hukumomin Rogo, Bagwai da Bebeji da ƙarin watanni uku.

Haka kuma, majalisar ta ƙara wa kwamitin da ke binciken zarge-zargen da ake yi wa shugabannin wa’adin watanni uku domin kammala aikinsa.

Sakataren yaɗa labaran majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

A cewar sanarwar, majalisar ta amince da ƙarin wa’adin dakatarwar shugabannin da kuma na kwamitin binciken zarge-zargen da ake yi musu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments