Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya ƙalubalanci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da su fafata a gasar karatun Alƙur’ani mai girma bayan dawowarsa daga ƙasar Saudiyya.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Melaye ya bayyana ƙalubalen ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, inda ya ce a shirye yake ya yi gasar da shugaban ƙasar wajen karanta ko ambaton ayoyin Alƙur’ani.
A cikin saƙon, tsohon sanatan ya ce: “Yanzu da Alhaji Bola Tinubu yake ƙasar Saudiyya domin gudanar da Umrah, da zarar ya dawo, ina ƙalubalantarsa da mu yi gasar karatun Alƙur’ani mai girma tsakanina da shi. Ai Allah ba abin wasa ba ne.”
Ƙalubalen na Melaye ya zo ne bayan ziyarar da Shugaba Tinubu ya kai ƙasar Saudiyya domin gudanar da Umrah, inda kuma aka ba shi damar shiga cikin Ƙa’aba.