Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya dakatar da duk wani shiri na ƙara ko sake duba kuɗin lasisin gidajen rediyo da talabijin har sai baba-ta-gani.
Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da tawagar ƙungiyar masu gidajen rediyo da talabijin ta Najeriya (BON), ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dr Tony Akiotu, a Abuja ranar Litinin.
Ministan ya ce matakin na da nufin rage ƙalubalen da masana’antar ke fuskanta, musamman tsadar gudanar da ayyuka. Ya kuma umarci Hukumar NBC da ta tabbatar da bin umarnin tare da gaggauta duba dokar kula da harkokin yaɗa labarai.
Dangane da shirin DSO, Idris ya yi alƙawarin shirya taron masu ruwa da tsaki domin warware matsalolin da suka rage. Ya kuma ce ya umarci ARCON da ta tabbatar da biyan kuɗin tallace-tallace cikin kwanaki 45.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta tattauna kan samun rancen kuɗi cikin sauƙi da rabon mitocin sadarwa. A nasa jawabin, shugaban BON, Dr Tony Akiotu, ya yaba wa ministan, amma ya jero ƙalubalen masana’antar da suka haɗa da tsadar aiki, kuɗin lasisi da rashin sauƙin samun tallafin kuɗi.