Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alƙawarin samar da tsayayyar wutar lantarki a faɗin ƙasar, yana mai cewa gwamnatinsa na da shirin tabbatar da samun wutar da al’umma za su iya dogaro da ita.
Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen samar da ingantacciyar wutar lantarki, maimakon ci gaba da tsarin sayar da kamfanonin wutar lantarki gaba ɗaya.
Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin gangamin yaƙin neman zaɓen sake zaɓensa da aka gudanar a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
Gidan Talabijin na NTA ne ya ruwaito kalaman shugaban ƙasar a yayin gangamin.