An kama wani da ake zargi da garkuwa da mutane, mai suna Mukaila Iliyasu, a lokacin da yake karɓar kuɗin fansa naira 200,000 a Akwaba, ƙaramar hukumar Eggon ta jihar Nasarawa.
An kama shi ne bayan jami’an DSS sun sanar da sojoji cewa ya yi barazanar sace wata mata idan ba ta biya shi kuɗin ba.
Domin cafke shi, wani soja ya yi basaja, ya yi kamar shi ne wanda aka tura domin kai kuɗin fansar, inda aka cafke wanda ake zargin yayin karɓar kuɗin.
Bayan kama shi, an miƙa Iliyasu ga jami’an DSS domin ci gaba da bincike da yiwuwar gurfanar da shi a kotu.
Kwamandan Operation Whirl Stroke, Manjo Janar Moses Kolo Gara, ya yaba wa jami’an tsaro bisa haɗin gwiwarsu, tare da kira gare su da su ƙarfafa musayar bayanan sirri domin yaƙi da garkuwa da mutane.