Wani kwamiti mai zaman kansa da ya binciki mutuwar mutane 33 a hannun hukumar NSCDC a jihar Neja ya gano cewa cunkoso, rashin isasshen iska, tsananin zafi da rashin ruwa ne suka haddasa mutuwarsu.
Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Jonathan Kure, tsohon mataimakin darakta-janar na DSS, ya ce mutuwar waɗanda ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba abin da za a iya kauce wa ne, musamman ganin cewa sun riƙa neman taimako amma ba a kula da su ba.
Rahoton ya kuma gano cewa an kama mutanen tare da tsare su ba tare da ingantaccen shiri da izini ba, yana mai watsi da bayanin farko na jami’an NSCDC cewa wata cuta ce ta haddasa mutuwar.
Kwamitin ya ba da shawarar korar jami’an da aka samu da hannu a lamarin tare da gurfanar da su a kotu. Ya kuma buƙaci gwamnati ta biya iyalan mamatan diyya, ta tallafa wa karatun ’ya’yansu, tare da samar da kulawar lafiya ga waɗanda abin ya shafa.
Haka kuma, ya buƙaci gwamnati ta bayar da uzuri a hukumance tare da inganta wuraren tsare mutane, horar da jami’an tsaro da kuma ƙarfafa tsarin sa ido domin kare haƙƙin waɗanda ake tsare da su.
Rahoton ya jaddada cewa kowane mutum yana da haƙƙin rayuwa da kariyar doka, ko da yana hannun jami’an tsaro. Ya kuma buƙaci a sake duba tsarin ayyukan NSCDC a faɗin ƙasar domin hana sake faruwar irin wannan mummunan lamari.