Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiMutane miliyan 33.5 a jihohi 26 za su fuskanci matsalar ƙarancin abinci...

Mutane miliyan 33.5 a jihohi 26 za su fuskanci matsalar ƙarancin abinci a 2027 – Rahoto

Wani rahoto ya yi hasashen cewa mutane miliyan 33.5, ciki har da waɗanda rikice-rikice suka raba da muhallansu, a jihohi 26 da Babban Birnin Tarayya Abuja za su fuskanci matsananciyar ƙarancin abinci da rashin isasshen abinci mai gina jiki tsakanin Yuni zuwa Agusta 2027.

Wani rahoto ya yi hasashen cewa mutane miliyan 33.5, ciki har da waɗanda rikice-rikice suka raba da muhallansu, a jihohi 26 da Babban Birnin Tarayya Abuja za su fuskanci matsananciyar ƙarancin abinci da rashin isasshen abinci mai gina jiki tsakanin Yuni zuwa Agusta 2027.

Rahoton na baya-bayan nan na Cadre Harmonisé ya bayyana hakan ne yayin taron gabatar da sakamakon bincike da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a.

Rahoton ya kuma nuna cewa mutane miliyan 26.8 a waɗannan jihohi da Abuja suna fuskantar matsalar ƙarancin abinci a halin yanzu, tsakanin Oktoba da Disamba 2026.

Gwamnatin tarayya ce ta haɗa rahoton ta hannun Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Abinci, tare da haɗin gwiwar Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), jihohi da sauran masu tallafawa.

Rahoton ya danganta matsalar da rikice-rikice da rashin tsaro, tashin farashin man fetur da abinci, sauyin yanayi da hauhawar farashin kayayyaki, waɗanda ke kawo cikas ga noma, rarraba abinci da ƙarfin sayen jama’a.

Wakilin FAO a Najeriya da ECOWAS, Dakta Hussein Gadain, ya ce Najeriya na da babbar damar samar da isasshen abinci, amma rashin tsaro, matsin tattalin arziki da sauyin yanayi na ci gaba da kawo ƙalubale. Ya jaddada muhimmancin tallafin abinci, taimakon kuɗi da shirye-shiryen farfaɗo da hanyoyin samun abin dogaro domin kare al’ummomin da suka fi fuskantar barazanar yunwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments