Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tarayya za ta riƙa bai wa talakawa tallafin Naira 50,000 duk...

Gwamnatin Tarayya za ta riƙa bai wa talakawa tallafin Naira 50,000 duk wata

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin fara bai wa iyalai masu fama da matsanancin talauci tallafin kuɗi naira 50,000 duk wata, domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa.

Ministan Jinƙai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce za a gudanar da rabon kuɗin ƙarƙashin shirin National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI).

Ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya ƙaddamar da shirin domin tallafa wa miliyoyin ’yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar matsin tattalin arziki.

A cewar sanarwar, an ƙirƙiri shirin ne sakamakon hauhawar farashin kayan abinci a duniya, wanda ke ƙara jefa iyalai cikin mawuyacin hali na tattalin arziki.

Sanarwar ta ƙara da cewa waɗanda za su ci gajiyar tallafin za su samu saƙon tes daga hukumar da ke kula da shirin domin neman amincewarsu kafin a tura kuɗin kai tsaye zuwa asusun bankinsu ko walat ɗin wayarsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments