Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar ADC ta soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yawan rancen kuɗin da take karɓa, tana mai cewa har yanzu ba a ga ayyukan more rayuwa da suka dace da yawan bashin da ƙasar ta tara ba.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na majalisar, Kola Ologbondiyan, ya fitar a Abuja, ADC ta bayyana kalaman da aka danganta da Shugaba Tinubu, ta bakin mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, cewa abin dubawa shi ne abin da ake ginawa ba yawan bashin da ake karɓa ba, a matsayin abin da ya ɓata mata rai.
Majalisar ta ƙalubalanci Shugaba Tinubu da ya bayyana manyan ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar da kuɗaɗen bashin da ta karɓa tun hawansa mulki a shekarar 2023.
Ologbondiyan ya yi zargin cewa ɗaya daga cikin ayyukan da suka fi fitowa fili a ɓangaren samar da wutar lantarki shi ne gonar hasken rana da aka girka domin samar da wuta a Fadar Shugaban Ƙasa, yayin da miliyoyin ’yan Najeriya ke ci gaba da fama da ƙarancin wutar lantarki.
Ya kuma yi iƙirarin cewa wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin ke tallatawa, kamar babbar hanyar Lagos zuwa Calabar, hanyar Sokoto zuwa Badagry da sauran manyan ayyuka, ba su kai matakin ci gaba da ake nunawa a kafafen yaɗa labarai ba.
Haka kuma, ADC ta soki jinkirin kammala aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano, tana mai cewa aikin da aka bayar sama da shekaru takwas da suka gabata har yanzu yana ci gaba da jawo damuwa ga masu ababen hawa.
Sanarwar ta ƙara da cewa ’yan Najeriya na fama da tsadar rayuwa, yunwa da matsalar tsaro, yayin da gwamnatin ke mayar da hankali kan tallata nasarorinta.
Ta kuma buƙaci ƙasashen duniya da hukumomin ba da lamuni su ƙara sanya ido kan yadda ake karɓa da kashe bashin Najeriya.
Daga bisani, ADC ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta ƙara taka rawa wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkokin karɓar bashi, maimakon amincewa da duk buƙatar rance da gwamnati ta gabatar.