Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiMajalisar wakilai ta gayyaci shugaban INEC kan shirye-shiryen zaɓe

Majalisar wakilai ta gayyaci shugaban INEC kan shirye-shiryen zaɓe

Majalisar wakilan Najeriya ta bai wa shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Joash Amupitan, wa’adin kwanaki bakwai na zaman majalisa domin ya yi wa kwamitin harkokin zaɓe bayani kan shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

Majalisar wakilan Najeriya ta bai wa shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Joash Amupitan, wa’adin kwanaki bakwai na zaman majalisa domin ya yi wa kwamitin harkokin zaɓe bayani kan shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

Matakin ya biyo bayan ƙudurin da ’yan majalisa Mansur Manu Soro da Abdussamad Dasuki suka gabatar, inda suka nemi a tantance shirye-shiryen hukumar. Sai dai Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu, ya nemi shugaban INEC ya bayyana a gaban kwamitin maimakon majalisar baki ɗaya, matakin da Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen, ya goyi baya.

Majalisar ta buƙaci INEC ta yi bayani kan rajistar masu zaɓe, samarwa da rarraba katunan zaɓe (PVC), amfani da fasahar BVAS da IReV, kayan aikin zaɓe, horar da ma’aikata, tsaro da kuɗaɗen gudanar da zaɓe.

’Yan majalisar sun kuma nuna damuwa kan matsalolin cibiyoyin rajistar masu zaɓe, ciki har da ƙarancin kayan aiki da ma’aikata, matsalolin sadarwa da dogon lokacin jira. Sun ce dole ne a magance matsalolin domin kada su hana matasa, mazauna karkara, ɗalibai da masu buƙata ta musamman yin rajista.

Majalisar ta ce sahihanci da amincewar jama’a ga zaɓen 2027 za su dogara ne kan shirin INEC, musamman ta fuskar tsaro, fasaha da gudanar da zaɓe. Ta kuma buƙaci hukumar ta yi amfani da darussan da aka koya daga zaɓen gwamnan Ekiti wajen inganta shirye-shiryenta, yayin da aka miƙa ƙudurin ga kwamitin harkokin zaɓe domin ci gaba da aiki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments