Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiMai ba Gwamnan Kano shawara ya naɗa ɗansa shugaban ma’aikatansa

Mai ba Gwamnan Kano shawara ya naɗa ɗansa shugaban ma’aikatansa

Ahmad Aruwa, mai ba Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, shawara kan yaɗa labarai, ya naɗa ɗansa, Aliyu Ahmed, a matsayin shugaban ma’aikatansa (Chief of Staff).

Ahmad Aruwa, mai ba Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, shawara kan yaɗa labarai, ya naɗa ɗansa, Aliyu Ahmed, a matsayin shugaban ma’aikatansa (Chief of Staff).

An sanar da naɗin ne ranar Talata, 27 ga Oktoba, 2026, tare da naɗin wasu mutum huɗu zuwa muƙamai daban-daban.

Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Habibu Liman a matsayin sakatare na musamman, Adamu Mai Salati a matsayin jami’in kula da ladabi da tarbar baƙi, Isa Ahmed Don a matsayin Darakta-Janar na yaɗa labarai da sadarwa, da Musa Muhammad Daurawa a matsayin mataimaki na musamman.

Da yake jawabi bayan karɓar takardar naɗinsa, Aruwa ya yi alƙawarin yin aiki tuƙuru, tare da nuna biyayya da jajircewa domin tabbatar da amincewar da gwamnan ya nuna masa.

Ya jaddada cewa Abba Kabir Yusuf ne jagoransa da shugaban siyasarsa, yana mai cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen tallafa masa da nasarar gwamnatinsa.

Aruwa ya kuma yaba wa tawagarsa ta yaɗa labarai bisa goyon baya da jajircewa, tare da bayyana kwarin gwiwar cewa za su ci gaba da aiki tare wajen wayar da kan jama’a game da manufofi, shirye-shirye da nasarorin gwamnatin jihar Kano.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments