Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabaraiKotu saka ranar yanke hukunci kan karar El-Rufai ta neman diyyar Naira...

Kotu saka ranar yanke hukunci kan karar El-Rufai ta neman diyyar Naira biliyan daya

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 2 ga Disamba, 2026, domin yanke hukunci kan ƙarar neman diyyar Naira biliyan ɗaya da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa El-Rufai ya shigar da ƙarar ne a kan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC, Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta sanya ranar yanke hukuncin, bayan lauyoyin ɓangarorin da ke shari’ar sun gabatar tare da amincewa da takardun hujjojin da suka shigar gaban kotu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments