Friday, November 6, 2026
HomeKasuwanciWasu ’yan Najeriya na kashe kashi 120 cikin 100 na kuɗin shigarsu...

Wasu ’yan Najeriya na kashe kashi 120 cikin 100 na kuɗin shigarsu wajen sayen abinci – Ministan Kudi

Ministan kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin Najeriya, Taiwo Oyedele, ya ce wasu ’yan Najeriya na kashe kuɗin da ya kai kashi 120 cikin 100 na abin da suke samu wajen sayen abinci, lamarin da ke tilasta musu karɓar bashi ko dogaro da ’yan uwa.

Ministan kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin Najeriya, Taiwo Oyedele, ya ce wasu ’yan Najeriya na kashe kuɗin da ya kai kashi 120 cikin 100 na abin da suke samu wajen sayen abinci, lamarin da ke tilasta musu karɓar bashi ko dogaro da ’yan uwa.

Oyedele ya bayyana hakan ne yayin wani taro a Chatham House da ke Landan, inda ya ce wani binciken gwamnati ya nuna cewa kuɗin abinci ya zarce kuɗin shigar wasu iyalai.

Ya ce duk da raguwar hauhawar farashin kayayyaki, farashin abinci na ci gaba da zama babbar matsala, inda hauhawar farashin abinci ya kai kashi 19.6 cikin 100 a watan Satumba.

Ministan ya danganta tsadar abinci da ƙarancin amfanin gona, asarar amfanin gona bayan girbi, rashin ingantattun wuraren ajiya, tsadar sufuri da rashin tsaro a yankunan noma. Ya ce ana iya rasa har kashi 60 cikin 100 na tumatir bayan girbi.

Ya bayyana cewa gwamnati na zuba jari a fasahar noma, ban-ruwa, wuraren ajiya da tallafin kuɗi ga manoma. Ya kuma ce shirin tallafin kuɗi kai tsaye na gwamnati ya kai ga gidaje sama da miliyan 10.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments