Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiGwamnan Katsina ya umarci gudanar da bincike kan hallaka Sheikh Masussuka

Gwamnan Katsina ya umarci gudanar da bincike kan hallaka Sheikh Masussuka

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan kisan Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, domin gano waɗanda suka aikata laifin da kuma gurfanar da su a gaban kotu.

Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026.

Wasu ’yan bindiga da ke kan babura sun kashe Sheikh Masussuka tare da wani mutum a ƙofar gidansa da ke Dutsin-Ma, a daren Litinin.

Gwamna Radda ya buƙaci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi domin gano waɗanda suka aikata kisan tare da tabbatar da an gurfanar da su a gaban kotu.

Haka kuma, gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, tare da ba hukumomin tsaro haɗin kai da kuma bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gudanar da binciken.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments