Ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya soki Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ba shi da ƙarfin jagorantar Najeriya, don haka ya kamata ya bar mulki a 2027.
Obi ya bayyana hakan ne a Abuja yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen NDC, inda ya zargi gwamnatin APC da ta’azzara talauci, rashin aikin yi, cin hanci da rashawa da matsalar tsaro.
Ya ce Najeriya na buƙatar shugaba mai ƙudurin magance matsalolin jama’a, maimakon ɗora wa wasu laifi.
Maganganunsa sun biyo bayan sanarwar Tinubu cewa ba zai halarci dukkan gangamin yaƙin neman zaɓen APC ba, domin mayar da hankali kan ayyukan gwamnati. Jadawalin jam’iyyar ya nuna zai halarci gangami a jihohi 12 da Abuja.
Obi ya kuma soki yadda Tinubu ya fara yaƙin neman zaɓen wa’adi na biyu ba tare da, a cewarsa, ya yi cikakken bayani kan kuɗaɗen bashin da aka karɓa da kasafin kuɗaɗen 2023 zuwa 2025 ba.
Ya yi alƙawarin cewa idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan magance matsalolin ƙasa da yaƙi da cin hanci. Sai dai APC ta kare matakin Tinubu, tana mai cewa babu dokar da ta wajabta wa ɗan takarar shugaban ƙasa ziyartar dukkan jihohi 36.