Kotun Tarayya da ke Court Road a jihar Kano ta yi watsi da ƙarar Hon. Sani Maidaji da ya shigar kan Rt. Hon. Engr. Hamisu Ibrahim Chidari, tare da tabbatar da Chidari a matsayin ɗan takarar Jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar tarayya ta Danbatta da Makoda a zaɓen 2027.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan nazarin ƙarar da Maidaji ya shigar, inda ya ƙalubalanci sahihancin takarar Chidari a ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC.
Hukuncin da aka zartar yau Talata ya tabbatar da matsayin Chidari a matsayin ɗan takarar jam’iyyar mai neman wakiltar al’ummar ƙananan hukumomin Danbatta da Makoda a Majalisar Wakilai ta Tarayya a zaɓen shekarar 2027.
Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaɓen 2027, inda ake samun takun-saka da ƙalubale kan zaɓen ’yan takara a wasu jam’iyyun siyasa.
Al Yusuf, daya daga cikin lauyoyin Hon. Chidari, da ya yi magana bayan ya bayyana cewa hukuncin kotun ya tabbatar da cewa bangare shari’a ya yi bakin kokarinsa wajen tabbatar da gaskiya da adalci.
A cewarsa, tun lokacin da aka fara shari’ar ake kai kawo har aka samu nasara.
Al Yusuf ya ce:
“Mun gamsu da hukuncin da Alkali ya yi. Allah ya taimaka mi shi.”
Maidaji ya yi karar Hon. Chidari, hukumar zabe ta kasa, INEC da jam’iyyar APC game da zaben fitar da gwani da aka gudanar.
Daga cikin zarge-zargen da ya yi ya bayyana cewa an canja wajen gudanar da zaben ba tare da an sanar musu ba.
Sai dai kotun ta yi watsi da karar tare da bayyana cewa Maidaji ba shi hujjoji game da zarge-zargen.
Wannan hukunci ta kara tabbatar da Hon. Chidari a matsayin Dan takarar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.