Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabaraiSERAP ta kai gwamnatin Tinubu kara kotun ECOWAS kan kuɗin tallafin talakawa

SERAP ta kai gwamnatin Tinubu kara kotun ECOWAS kan kuɗin tallafin talakawa

Ƙungiyar SERAP mai fafutukar kare haƙƙin jama’a da tabbatar da gaskiya ta shigar da ƙara a gaban Kotun ECOWAS kan zargin rashin bayyana yadda aka kashe naira biliyan 78.8 da aka ware domin tallafa wa talakawa ta hanyar shirin ba da tallafin kuɗi.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, a cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya fitar ranar Lahadi, ƙungiyar ta ce zarge-zargen sun shafi Ma’aikatar Jinƙai da Rage Talauci, Ofishin Kula da Biyan Kuɗi da kuma Ofishin Daidaita Shirye-shiryen Tallafin Jama’a.

SERAP ta ce an bayyana waɗannan matsaloli ne a cikin rahoton babban mai binciken kuɗaɗen gwamnatin tarayya na shekarar 2024, wanda aka wallafa a ranar 7 ga Agusta, 2026.

A cewar rahoton, an nemi ƙarin bayani kan yadda aka kashe naira biliyan 33.75 da aka ce an raba wa gidaje sama da miliyan 3.2 a jihohi 35 a shekarar 2023, saboda rashin cikakkun bayanan da za su tabbatar da biyan kuɗaɗen.

Haka kuma, rahoton ya nuna cewa an biya naira biliyan 36.74 ba tare da tantance kuɗaɗen kafin biyan su ba, yayin da aka gano wasu kashe-kashe na naira biliyan 4.6 da ba su da isassun takardun shaida.

Ƙungiyar SERAP ta buƙaci kotun ta umarci gwamnati da ta bayyana cikakken bayani kan kuɗaɗen, ta gudanar da bincike mai zaman kansa, tare da dawo da duk kuɗin da aka tabbatar an karkatar ko aka kashe ba bisa ƙa’ida ba.

Ta kuma nemi a ɗauki matakin da ya dace kan duk waɗanda aka samu da laifi.

Sai dai, zarge-zargen da SERAP ta gabatar ba su zama hujjar cewa an tabbatar da karkatar da kuɗaɗen ba, kuma ana buƙatar bincike domin tabbatar da abin da ya faru.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments