Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiKarancin ma’aikatan jinya na barazana ga kula da masu cutar kansa a...

Karancin ma’aikatan jinya na barazana ga kula da masu cutar kansa a Najeriya

Karancin ma’aikatan jinya na Masana aikin jinya sun yi gargaɗin cewa ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan kula da masu cutar kansa na kawo cikas ga jinya a Najeriya. Sun buƙaci gwamnati ta inganta walwalarsu da damar samun horo.

Karancin ma’aikatan jinya na Masana aikin jinya sun yi gargaɗin cewa ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan kula da masu cutar kansa na kawo cikas ga jinya a Najeriya. Sun buƙaci gwamnati ta inganta walwalarsu da damar samun horo.

A cewar NICRAT, Najeriya na samun sabbin masu cutar kansa tsakanin 102,000 zuwa 127,763 a kowace shekara, yayin da mutane 72,000 zuwa 79,542 ke mutuwa sakamakon cutar.

Farfesa Khadijat Musah ta kiyasta cewa ƙwararrun ma’aikatan jinya a fannin cutar kansa kusan 300 ne a ƙasar. Ta ce ƙaurarsu zuwa ƙasashen waje na ƙara ta’azzara ƙarancin ma’aikatan.

Musah ta ce cibiyoyi biyu ne kawai ke horas da ma’aikatan jinya a wannan fanni a Najeriya. Ta buƙaci gwamnati ta inganta walwalar ma’aikatan tare da ƙara damar samun ƙarin horo.

Mataimakiyar shugabar Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya Masu Kula da Cutar Kansa ta Najeriya, Fatima Adam, ta ce ƙwararrun ma’aikatan jinya muhimmin ɓangare ne na kula da masu cutar. Ita ma Nanre Mampak ta buƙaci gwamnati ta shigar da ma’aikatan jinya cikin yanke shawarar da ta shafi harkokin lafiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments