Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabaraiDuk ɗan Arewa mai neman shugabancin Najeriya a 2027 maƙiyin yankin ne...

Duk ɗan Arewa mai neman shugabancin Najeriya a 2027 maƙiyin yankin ne – George Akume

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ya ce duk ɗan Arewa da ke neman shugabancin Najeriya a zaɓen 2027 maƙiyin yankin ne, yana mai cewa lokacin Arewa na komawa kan mulki shi ne 2031.

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ya ce duk ɗan Arewa da ke neman shugabancin Najeriya a zaɓen 2027 maƙiyin yankin ne, yana mai cewa lokacin Arewa na komawa kan mulki shi ne 2031.

Akume ya bayyana hakan ne ranar Asabar a wani taro da ’yan asalin Benue da ke zaune a Kaduna, a ranar da APC ta ƙaddamar da kamfen ɗin neman sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.

Ya ce an cimma yarjejeniyar karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu a Kaduna domin kiyaye haɗin kan Najeriya. Saboda haka, ya buƙaci ’yan Arewa su goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027.

Akume ya gargaɗi ’yan Arewa da kada su bari burin siyasar wasu mutane ya raba kan yankin ko ya raunana tasirinsa. Ya kuma ce bai kamata a bari siyasa ta haddasa rarrabuwar kai bisa addini ko muradun kansu ba.

Da yake kare Tinubu, Akume ya ce shugaban na yin adalci wajen naɗe-naɗen mukamai, tare da gudanar da ayyukan raya ƙasa a Benue da sauran jihohi. Ya kuma soki Atiku Abubakar kan matsayinsa game da cire tallafin man fetur.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments