Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiBa zan yi wa kowa kamfen ba – Sheikh Daurawa

Ba zan yi wa kowa kamfen ba – Sheikh Daurawa

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa shi ba ɗan siyasa ba ne kuma ba zai yi wa wani ɗan takara kamfen ba, sai dai yana fatan Allah Ya ba duk wanda zai tabbatar da adalci da kare haƙƙin talakawa nasara.

Nasara Radio ta rawaito cewa malamin ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Asabar.

A cikin saƙon, Sheikh Daurawa ya ce: “Ni ba ɗan siyasa ba ne, kuma ba zan yi wa kowa kamfen ba. Amma ina fata duk wanda zai tabbatar da adalci, ya tausaya wa talakawa, ya kare haƙƙinsu, kuma ya yi aiki domin inganta rayuwarsu, Allah Ya ba shi nasara.”

Malamin ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba Najeriya shugabanni masu gaskiya, riƙon amana da tsoronSa, waɗanda za su fifita buƙatun al’umma a kan nasu.

Ya ce: “Allah Ya ba mu shugabanni masu gaskiya, riƙon amana da tsoronsa, waɗanda za su fifita buƙatun al’umma a kan buƙatunsu. Amin ya Rabbal Alamin.”

Wannan furuci na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan bayyanar sunan Sheikh Daurawa a cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a Kano, lamarin da ya jawo hankali kan matsayarsa game da siyasa da kamfen.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments