Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa al’ummar Arewa za su nuna godiyarsu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hanyar ba shi ƙuri’u a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Uba Sani ya bayyana hakan ne yayin da yake nuna goyon bayansa ga ƙoƙarin Tinubu na neman wa’adi na biyu a kan mulki.
Gwamnan ya nuna kwarin gwiwar cewa al’ummar Arewa za su tuna da abubuwan da gwamnatin Tinubu ta yi musu, su kuma mayar da martani ta hanyar goyon bayansa a zaɓe mai zuwa.
Sai dai wannan furuci na zuwa ne a lokacin da tattalin arziki, tsadar rayuwa da matsalolin tsaro ke cikin muhimman batutuwan da ake tattaunawa a kansu gabanin zaɓen 2027.