Tuesday, October 20, 2026
HomeLabaraiLabarai“Ban yi nadamar cire tallafin man fetur ba” – Tinubu

“Ban yi nadamar cire tallafin man fetur ba” – Tinubu

Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa bai yi nadamar cire tallafin man fetur ba, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta mayar da ƙasar tsarin tallafin man fetur ba.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin wani taro mai taken “Together till 2027: An Evening with Original City Boy”, wanda ƙungiyoyin City Boy Movement da Relax-Tinubu-Is-Fixing-Nigeria suka shirya a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen yaƙin neman sake zaɓensa a 2027.

Shugaban ya ce kafin cire tallafin, Najeriya na fuskantar barazanar durƙushewar tattalin arziki.

Ya kuma soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan alƙawarinsa na dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.

Tinubu ya kwatanta cire tallafin da tafiyar Annabi Musa daga Masar, yana mai cewa Najeriya ba za ta koma tsarin da ta bar baya ba.

Ya amince cewa shekaru uku da suka gabata sun kasance masu wahala ga ’yan Najeriya, amma ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakai masu tsauri domin inganta tattalin arzikin ƙasar.

Haka kuma, Tinubu ya bayyana cewa sama da ɗalibai miliyan ɗaya sun amfana da tallafin kuɗin karatu ta Asusun Ba da Lamunin Karatu ga Ɗalibai (NELFUND), yana mai cewa bai yi nadamar kafa asusun ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments