Fitaccen attajirin masana’antu a Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana cewa gara a daure shi a kurkuku da a hana shi amfani da wayarsa ta hannu.
Dangote ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Legas, inda ya ƙaddamar da shirinsa na Vision 2030. An tambaye shi ko zai fi son ya yi mako guda ba tare da wayarsa ba ko kuma a hana shi amfani da jirginsa na kashin kansa.
A cikin amsarsa, Dangote ya ce zai fi masa sauƙi a kai shi kurkuku da a ƙwace masa waya. Ya jaddada cewai wayarsa na da matuƙar muhimmanci a rayuwarsa.
Attajirin ya bayyana cewa yana da lambobin waya sama da 13,000 a cikin wayarsa. Ya ce yana da yawan lambobin ne saboda yana hulɗa da mutane da dama a harkokin kasuwanci da rayuwar yau da kullum.
Dangote ya kuma ce ba kasafai yake toshe lambobin mutane a wayarsa ba. Shi ne shugaban rukunin kamfanonin Dangote, wanda ke da manyan harkokin kasuwanci da suka haɗa da samar da siminti, takin zamani da tace man fetur.